Ministar Abuja Mariya Bunkure ta fita zakka cikin masu mukaman gwamnatin tarayya a Kano – Hon. Abba Kawu

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Mataimakin na musamman kan aiyuka na musamman ga Karamar ministar babban birnin tarayya Abuja Hon. Abba Kawu ya bugi girjin cewa ministar Abuja Dr. Mariya Mahmoud Bunkure tana cikin mutane uku masu mukamin gwamnatin tarayya da suka fi kishin kano da kanawa.

” A ko da yaushe mai girma minista bata da wata magana sai ta yaya za’a taimaki al’umma musamman mata da mata saboda su ne kashin bayan cigaban kowacce al’umma, hakan tasa a kowanne lokaci ta ke shiga cikin mutane don jin koken su domin ta taimaka musu”.

Talla

Hon. Abba Kawu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da wakilin jaridar kadaura24 a Kano.

Yace tun kafin Dr. Mariya ta sami mukamin Ministar Abuja take shiga lungu da sako na Karamar hukumar Bunkure take tallafawa al’umma, don haka yanzu da ta zama Minista abun kara fadada shi ta yi har zuwa sassan kano daban-daban, saboda tausayi da take da shi.

“Game da maganar aikin da Shugaban Kasa Tinubu ya dora mata kuwa, Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta tsaya tsayin daka domin ganin ta sauke nauyin da aka dora mata, domin tana aiki ne ba dare ba rana wajen ganin ta aikin ta yadda ya dace”. Hon. Abba Kawu

Kansilolin Bunkure da Wata Gidauniyar Kiwon Lafiya Sun Karrama Ministar Abuja Dr. Mariya

” Jajirtacciya ce da bata da kasala wajen aiki, hakan tasa al’ummar babban birnin tarayya Abuja suke yaba mata saboda yadda take sadaukar da lokacin ta wajen hidimta musu a koda yaushe, wanda hakan ya sa take ta samun lambobin yabo daga kungiyoyin daban-daban domin yaba mata da kara mata kwarin gwiwar cigaba aikin ta yadda ya dace”.

Gaskiyar Batu Kan Ranar Yanke Hukuncin Shari’ar Gwamnan Kano

Babban mataimaki ga Ministar ya kuma bukaci al’ummar yankin Rano Kibiya da Bunkure da ma jihar kano baki daya da su kara dagewa da yiwa ministar addu’o’in Allah ya cigaba da dafa mata wajen sauke nauyin da Shugaban Kasa Tinubu ya dora mata, sannan ya bata ikon cigaba da tallafawa al’umma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...