Dan Jaridar Da Ya Tona Asirin Digirin Dan Kwatano Ya Koka

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Dan jaridar na wanda ya tona asiri yadda ake digirin wata biyu a Kasar Benin, Umar Audu, ya koka cewa yana tsoron halin da zai iya fadawa gane da lafiyarsa da rayuwarsa, saboda yadda ya bankado badakalar da ake yi wajen karatu a Togo da Benin.

Idan dai ba a manta ba, dan jaridar da ke bincike a jaridar Daily Nigeria, ya ruwaito a kwanan baya cewa ya samu takardar shaidar digiri a cikin makonni shida a wata jami’ar dake kasar Benin, sannan kuma ya shiga irin masu yiwa kasa hidima na Nigeria wato NYSC.

Dan jaridar ya bayyana cewa ya samu duka kwafi da satifiket na jami’ar Ecole Superieure de Gestion et de Technologies, Cotonou, Jamhuriyar Benin bayan makonni shida kawai.

Talla

A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels a jiya, ya bayyana cewa abin damuwa ne yadda tsarin tsaro yake a Najeriya, Inda ba za’a baiwa ‘yan jarida kwarin guiwar yin aikinsu ba tare da fargabar cin zarafi ba.

Da mai gabatar da shirin ya tambaye shi ko ya samu wata barazana bayan rahoton nasa, Umar Audu, ya bayyana cewa duk da cewa har yanzu bai samu wata barazana ba, amma tsoron hakan yasa ya daina shiga cikin mutane saboda kare lafiyarsa.

Hukumar Tace Fina-Fina ta Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Zargin da ake yiwa Jaruma Maryam Yahya

Ya ce: “Akwai damuwa da yawa daga abokai da ’yan uwa game da tsaro na. Sun damu kwarai da gaske kuma a matsayina na dan jarida, na yi imanin ya kamata a bar ni na gudanar da aikina ba tare da wata barazana ba.

“Wannan halin da ake ciki ya nuna irin al’ummar da muke rayuwa a ciki, inda ya kamata ‘yan jarida su rika gudanar da ayyukansu cikin lumana da kuma tabbatar da tsaron lafiyarsu.

Yan sanda sun kama likitan bogi dake zubar da ciki a Kano

“Ina so in yi amfani da wannan dama domin yin kira ga hukumomi da su tabbatar da bani kariya, duk da cewa a halin yanzu ina cikin wani wuri mai tsaro. Duk da haka, ba ni da tabbas game da abin da zai iya faruwa a nan gaba, saboda rahoton nawa ya zaga ko ina .

“Ina fata gwamnati ta ci gaba da taka-tsan-tsan kuma idan akwai wata barazana, zan tuntube su da gaggawa domin ganin na samu kariyar da ta dace.”

Da aka tambaye shi ko nawa ya kashe wajen sayen takardar digirin da yayi?, Umar ya ce: “Na kashe kusan Naira 600,000. Ban je kan iyakar Nigeria ba, Na ba jami’in shige da fice ne kawai ya taimaka min wajen samun fasfo na kungiyar ECOWAS da tambarin hukumar shige da fice ta Najeriya da Benien, wanda na kashe Naira 150,000.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...

Dan majalisa Bichi ya sake biyan kuɗin makarantar dalibai 121 masu karatun digiri na biyu da na digirin digirgir

Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Mazabar Bichi a Majalisar...