Daga Rahama Umar Kwaru
Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta kama wani matashi mai shekara 19 da zargin yi wa ‘yar uwarsa ciki a ƙaramar hukumar Tofa da kuma zargin haɗa baki wajen kashe ta.
Wata sanarwa da Kakakin rundunar SP Abdullahi Kiyawa ya aikowa kadaura24, ta ce runundar ta ce ta kama Ukasha Muhammed ne bayan ta samu rahoton cewa ya yi wa Amina Bala mai shekara 19 ciki, sannan ya kai ta wajen wani mai suna Chidera Ugwu don ya yi mata allurar zubar da cikin.

Sanarwar ta ce Mista Ugwu, wanda likitan boge ne, ya yi mata allura tare da ba ta wasu ƙwayoyin magani da zimmar zubar da cikin, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.
Da dumi-dumi: Tinubu ya fara fatali da manufofin Buhari
“An kama waɗanda ake zargin kuma sun amsa laifukan da ake zargin su da aikatawa,” in ji runudnar.

Ta ƙara da cewa da ma Ugwu ya saba yi wa mata masu ciki “allurar da ke kaiwa ga rasa rayukansu”.