Hukumar Tace Fina-Fina ta Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Zargin da ake yiwa Jaruma Maryam Yahya

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Hukumar tace fina-fina da daf’i ta jihar kano ta bayyana cewa ta wanke Jarumar masana’antar kannywood Maryam Yahaya bisa wani zargi da akai mata na rungumar wani saurayi a cikin wani bidiyo.

” An kawo mana korafi akan jaruma Maryam Yahaya kan wani bidiyo da ake yadawa a kafafen Sada Zumunta, Inda aka ga wani yana rungumar wata wacce ake zargin Maryam Yahaya ce, amma bayan mun gudanar da bincike mun gano cewa ba Maryam Yahaya ba ce a cikin bidiyon”.

Mai magana da yawun hukumar Abdullahi Sani Sulaiman ne ya bayyana hakan Yayin wata ganawa da yayi da freedom Radio dake kano.

Talla

Yace ban da aka Kai musu koken shugaban hukumar tace fina-fina ta jihar kano Abba El-Mustapha ya baiwa daraktan dake kula da Yan masana’antar kannywood damar gudanar da bincike don tabbatar da anyi adalci ga kowanne bangare.

 

” Bayan kammala binciken hukumar mu ta tabbatar da cewa Wacce ake zargin ba jaruma Maryam Yahaya ba ce, don haka muka ga dacewar mu fito mu shaidawa duniya cewa ba Maryam bace, saboda abun ya yadu da yawa bai dace mu yi shuru akan maganar ba”. Inji Abdullahi Sani Sulaiman

Gwamnan Kano Abba Kabir Ya Magantu Kan Batun Naushin Sakataren Gwamnati Baffa Bichi

Jami’in hulda da jama’a na hukumar ya bukaci al’ummar jihar kano da zu cigaba da baiwa hukumar hadin kai ta hanyar kai rahotannin abubunwan da suka ga ana yi a kannywood ba dai-dai ba, domin daukar matakin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...