Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama wata babbar mota makare da kwalaben barasa sama da 24,000.
Babban daraktan hukumar ta Hisbah ta jihar Kano, Abba Sufi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Lawan Ibrahim Fagge a yau Laraba a Kano.

Hukumar, wacce ta yi kamen a hanyar Zariya a Kano, ta kuma kama direban motar da wasu mutane biyu.
Da dumi-dumi: Tinubu ya fara fatali da manufofin Buhari
“Motar da ke dauke da kwalabe daban-daban na barasa sama da 24,000 an kwace daga hannun masu fasa kwaurinta a hanyar Zariya da tsakar dare.
“Jami’an Hisbah a jihar sun himmatu wajen aiwatar da manufar ba-sani-ba-sabo ga fasakwaurin barasa da sauran abubuwa masu sa maye a cikin jihar,” in ji shi.