Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya musa jita-jitar da ake yadawa na cewa sun yi dambe tsakaninsa da sakataren gwamnatin jihar Dr. Abdullahi Bappa Bichi.
Da yake jawabi yayin bikin rantsar da sabbin manyan sakatarorin gwamnati da masu ba da shawara na musamman a gidan gwamnati, Gwamnan ya bayyana cewa babu wani farfaganda da zai hana gwamnatinsa cimma burinta.

Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa nadin shugaban ma’aikatan jihar a matsayin mukaddashin SSG ba yana nufin an kori Baffa Bichi daga mukamin sa ba ne .
Yayin da yake magana kan yada labaran karya, Abba Kabir ya bayyana cewa, wadanda suke dauki siyasa a matsayin madogararsu ta rayuwa, su ne suke kirkiro jita-jita don tada hankulan da ba dole ba, amma kuma hakan su bai cimma ruwa ba .
Wakokin Kannywood 5 Da Suka Fi Shahara A 2023
Gwamna Yusuf, yace na bada rikon mukamin sakataren gwamnati ne saboda muhimmacin da mukamin yake da shi, ba zai yiwu a tafiyar da gwamnati a haka ba.
Gwamnan ya bada tabbacin idan Baffa Bichi ya samu sauki, to da zarar ya dawo zai cigaba da aikinsa.