Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Guda cikin masu neman shugabancin kungiyar dillalan man fetur ta kasa reshen jihar Kano wato IPMAN Alhaji Nasiru Garba Ali, ya sha alwashin matukar yan kungiyar suka zabe shi a matsayin Shugabansu zai yi duk mai yiyuwa wajen kare hakkokin su da ciyar da kungiyar gaba.
Alhaji Nasiru Garba Ali ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.
” Na dara sauran masu neman wannan kujera da akalla abubuwan guda shida, wadanda nayi Imani za su taimaka min waje magance duk wasu matsaloli da yan kungiyar mu suke fuskanta a ciki da wajen jihar kano”. Inji Alh. Nasiru Garba

Yace akwai bukatar kowanne Shugaba ya zamana yana da gogewa a sha’anin shugabancin wanda hakan yana sawa ya sami sauƙi wajen jagorantar mutanensa, ” na jima Ina kasancewa cikin shugabanci a bangarori daban-daban a kungiyoyi daban-daban, to zan yi amfani da gogewar wajen yin Shugabanci abun kwatance idan na zama Shugaban IPMAN reshen jihar Kano”.
” Na kasancewa a harkar Mai sama da shekaru 15 don haka nasan kalubalen da take fuskanta kuma nasan hanyoyin da zan bi domin warware matsalolin da ya’yan kungiyar mu suke fuskanta cikin sauƙi “. Inji Alhaji Nasiru Garba
Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya Sake Nada Masu Bashi Shawara guda 14
Alhaji Nasiru Garba Ali wanda shi ne shugaban kamfanin Mai na Garba Ali Nig. LMT. yace yana da tsare-tsare masu tarin yawa da zasu bashi damar samar da kyakyawan yanayi da damar gudanar da harkokin kasuwanci cikin walwala ba tare da tsangwama ba ga yan kungiyar IPMAN.
” Na yi matukar yarda da hadin kai domin yana kai al’umma ga cigaban mai dorewa, don haka idan na zama Shugaban IPMAN zan haɗa kai da duk masu ruwa da tsari a harkar mai domin samar da damammakin da zasu taimakemu wajen magance ƙalubalan da muke ciki “. Inji shi
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya Nada Karin Manyan Mataimaka 57
” Zamu yi aiki tukuru ta hanyar haɗa akai da Kwararru wadanda zasu taimaka mana wajen sake fito da managartan manufofin da zasu sa mu kyautata sana’ar mu , saukaka mana wajen biyan haraji da kuma samun kyakyawar alaka tsakanin mu da hukumomin da suke kula da mu don inganta sana’armu”.
Alhaji Nasiru Garba Ali ya bada tabbacin idan ya zama Shugaban IPMAN zai yi amfani da fasahar zamani wajen inganta harkokinsu da Kuma tabbatar da cewa ‘ya’yan kungiyar sun sami wani horo na musamman kan yadda zasu rika harkokin kasuwancinsu ta amfani da fasahar don gudun kada a bar su a baya.
Yace yana da yaƙinin ‘ya’yan kungiyar dillalan man fetur ta kasa reshen jihar Kano IPMAN ba zasu taba yin dana sanin zabar sa, hasali ma sai sun yi alfahari da jagorancin da zai yi musu.