Daga Sani Idris Maiwaya
Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Injiniya Abba Kabir Yusuf, ta rage kaso hamsin cikin ɗari (50%) na kuɗin makarantun gaba da sakandare mallakin jihar.
” A Yau ( jiya litinin) na sami ganawa da shugabannin manyan makarantun gaba da sakandire na jihar kano, inda na umarce su da su rage kuɗin makarantun da kaso 50 ba tare da bata lokaci ba”. Inji Abba Gida-gida

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a sashihin shafin sa na Facebook jin kadan bayan kammala ganawa da shugabannin manyan makarantun .
Bai Kamata Gwamnatin Kano ta yi Auren Zawarawa a Wannan Lokacin ba – Shitu Sani Marshall
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito dalibai musamman wadanda suke Karatu a jami’o’in gwamnatin tarayya suna ta kokawa da yadda aka Kara Kudin makarantun.
Wannan mataki dai na gwamnatin jihar kano zai taimaka matuka wajen saukakawa dalibai su yi karatu cikin sauƙi a jihar kano.
Ko a makon jiya ma sai da gwamnatin jihar kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani ya bada tabbacin rage yawan kudaden manyan makarantun dake jihar.