Muntari Muhammad Liti shi Yafi Dacewa ya Zama Shugaban Kasuwar Singa – Alh. Balarabe

Date:

Daga Ibrahim Sani Gama

 

Kungiyar ‘yan kasuwar singa karkashin Kungiyar (AMATA) ta jaddada goyan bayanta don tabbatar da an kawo managartan shirye-shirye da za su bunkasa harkokin ‘yan kasuwar ta hanyar tsayar da Muntari Mohammed Liti Kwasamgwami, a matsayin shugaban kasuwar a zaben dake tafe.

 

Sakataren Kungiyar na AMATA Alhaji Balarabe ne ya bayyana hakan a lokacin da yake kira ga matasa da ‘yan kasuwar da su marawa Muhammed Liti domin kawo sauyi da ci gaba mai dorewa a cikin kasuwar singa.

Talla

Yace, lokaci yayi da za’a sanya matasa masu kishi wajen ganin sun sami Shugabanci Kungiyar kasuwar singa gaba dayanta domin al’umma su san ana yi da su, musamman wajen kawo taimako daga gwamanati mai ci a halin yanzu.

Tinubu ya sake tura tawagar Malamai zuwa Jamhoriyyar Nijar

A jawabunsa dan takarar Shugabancin Kungiyar kasuwar singa Muntari Muhammad liti ya sha alwashin yin aiki kafada da kafada da manyan ‘yan kasuwa da kanana da matasa da sauran al’ummar Singa ta yadda za’a farfado da ita kamar lokutan da suka gabata.

 

Muntari Mohammed Liti Kwasamgwami, ya bayyana cewa, Akwai aikace aikace da ya sanya a gaba da zarar ya samu Darewa wannan Kujera ta Shugabancin Kungiyar kasuwar singa.

Shari’ar zaɓen gwamna: Kwankwaso, Gwamnan Kano, da Wasu Sunyi Addu’a ta Musamman Domin Neman Nasara

“Daga cikin Abubuwan da zan fara yi, akwai samar da magudanan ruwa domin kaucewa afkuwar ambaliyar da inganta rayuwar matasa, musamman leburori da kananan Yankasuwa Wadanda ke bukatar Tallafin jari daga hannun Gwamnatin jihar kano”. Inji Muntari Liti

 

Muhammed Liti Kwasamgwami, ya kara da cewa, akwai samar da tsaro da kare martabar dukkannin yan kasuwar da suke fuskantar matsaloli daga wasu Hukumomi babu gaira ba dalili ta hanyar cin mutuncinsu ba tare da an Tuntubi Hukumar gudanarwar Kasuwa ba.

Dantakarar yace,za kuma,su marawa yunkuri Gwamnati jihar kano baya na farfado da Tattalin arzikin kasuwanci ta hanyar Zamanantar da Al’amura yadda suka kamata.

Ya jaddada cewa, Gwamnan jihar kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa, Gwamnatinsa Dana da tsare tsare musu yawa ga Alummar jihar kano, musamman’ ‘Yankasuwa karkashin jagorancin Ma’aikatar kasuwanci ta ta jihar nan .

Yace, Kwamishinan Ma’aikatar kasuwanci da ciniki Abas Sani Abas, dan kasuwa ne daya san halin da ‘yan kasuwa suke ciki, kuma ya bayyana cewa, zai hada kai da kungiyoyin ‘yan kasuwa domin ciyar da kasuwanci gaba a fadin jihar kano da ma kasa baki daya.

Mohammed Liti yace, yawan kiraye-kiraye da al’ummar Singa suke yi masa a matsayin Da kungiyar Kwankwasiyya da Kungiyar (AMATA) ya ga dacewar ya fito domin bayar da tasa Gudunmawar ta hanyar Shugabantar Alumma da ma kasuwar singa Dingurungun.

Haka zalika, Dan takarar ya nemi hadin kan al’umma da suke kasuwanci ,manya da Dattijai da matasa maza da mata da su bashi hadin kan da ya kamata domin ganin an samu nasarar kawo sauyi mai nagarta ta kowanne fanni na kasuwar singa, duba da kasance jihar kano cibiya ce ta kasuwanci a fadin kasar nan da ma kasashen ketare.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...

Yadda Makarantar JSS Unguwa uku dake K/H Tarauni ta Zama mafakar shaye-shaye da yan daba

Daga Mubina Ahmad Galadanchi Wasu daga cikin al'ummar unguwar unguwa...