Daga Rukayya Abdullahi Maida
Daraktan yada labarai da hulda da jama’a na hukumar yi wa kasa hidima (NYSC), Eddy Megwa, ya bayyana cewa ministar fasaha da al’adu ta Nigeria, Hannatu Musawa, wadda a halin yanzu take yiwa kasa hidima na shekara guda, ta rike mukamin minista ba , haka ya sabawa dokar NYSC.
Da take magana da wakilin Daily trust ta wayar tarho, Megwa ta tabbatar da cewa ministar yanzu haka ta shafe watanni takwas tana aikin yiwa kasa hidima a babban birnin tarayya Abuja.

Ya bayyana cewa ya sabawa dokar NYSC duk wani dan bautar kasa ya karbi duk wani mukami na gwamnati har sai ya kammala hidimar shekara daya.
Tinubu ya sake tura tawagar Malamai zuwa Jamhoriyyar Nijar
Ya ce tun a shekarar 2001 aka tura Hannatu Musawa sanana ‘yan yiwa kasa hidima dake jihar Ebonyi, amma daga baya ta koma jihar Kaduna domin ci gaba da shirin.
Ya ce lokacin da ta koma Kaduna ne ta gudu ba ta kammala shirin ba.
Hotunan yadda Sabon Shatale-talen Kofar Gidan Gwamnatin Kano ya kasance
Megwa ya ce hukumar NYSC zata duba batun ta kuma ɗauki matakin da ya dace akan Hannatu musawa .