Gaza biyan diyya da gwamnatin Kano ta yi ne ya tsayar da aikin titin Gwarzo zuwa Katsina – Ma’aikatar Aiyuka ta Kasa

Date:

Daga Sani Danbala Gwarzo

 

Ma”aikatar aiyuka ta kasa ta dora alhakin tsayarwar aikin da gwamnatin tarayya take yi daga Kano zuwa Dayi dake jihar katsina akan gwamnatin jihar kano.

 

” Rashin biyan diyya masu gidaje da konakin da ke hanyar daga gwamnatin jihar kano shi ne babban abun da ya kawo tsaiko wajen kammala aikin akan lokaci, amma muna cigaba da bibiyar gwamnatin don ganin ta biya diyyar domin muma mu samu mu kammala aikin”.

Talla

Kadaura24 ta rawaito Shugaban ma’aikatar aiyuka ta kasa mai kula da aiyukan jihar kano Engr. Yahya baba Ali ne ya bayyana haka a yayin ganawa da manema labarai a ofishinsa dake babbar sakatariya gwamnatin tarayya a titin katsina dake Nan kano.

Cikakken bayanin yadda Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Abba Kabir Yusuf

Engr. baba Ali ya kuma kara da cewa yanayin damuna ma ya taimaka wajen Kara samun jinkirin aikin wanda aikin baya yuwuwa saboda kasa ta yi laushi.

Anasa bangaran shugaban kamfanin dake Kwangilar aikin titin gwarzo zuwa dayi Mr. Ben yace al’ummar yankin su daina zargin guduwa suka yi, domin yace har yanzu kayan aikin su suna nan a sansaninsu ba guduwa sukai ba .

Tinubu ya sake tura tawagar Malamai zuwa Jamhoriyyar Nijar

Mr. Ben ya kuma yi kira ga mazauna yankunan da aikin ya shafa dasu cigaba da basu cikakken hadin kai da goyon bayan, in Kuma suna da wani korafi to a sanar dasu don gyarawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Alhaji Aminu Dantata ya bar gibin da zai wuyar cikawa a Nigeria – Alhaji. Kabiru Sani Kwangila

Shugaban kamfanin gine-gine na SKY Alhaji Kabiru Sani Kwangila...

Sanarwa ta Musamman daga majalisar malaman Kano game da rasuwar Dantata

SANARWA MUHIMMIYA (GABATAR DA SALLATUL GA'IB) Assalamu Alaikum Warahmatullah, Sakamakon rasuwa...

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...