Za’a yi rigakafi a rijiyoyin dubu uku dake Karamar hukumar Bichi – Farfesa Yusuf Sabo

Date:

Daga Abubakar Lawan Bichi

 

Shugaban karamar hukumar Bichi, Ferfesa Yusuf Mohammed Sabo ya cewa gwamnatin jihar Kano ta amincewa Karamar hukumar ta fara aikin zuma rigarkafin chlorine a rijiyoyi kusan 3000 a mazabu 11 na karamar hukumar .

 

Shugaban karamar hukumar, wanda Likitane kuma Farfesa ne na fannin kananan halittu da kwayoyin cuta, ya ce za a gudanar da aikin ne da nufin hana yaduwar cututtuka masu yaduwa a cikin al’umma, a lokacin damina sakamakon yadda duk wata budaddiyar rijiya ke zama tushen ruwan sha a cikin al’umma.

 

Ya bayyana cewa za a sanyawa daukacin rijiyoyin dake karamar hukumar Bichi sinadarin chlorine a kokarin da ake na yaki da cututtuka masu yaduwa ta ruwa musamman kwalara.

Talla

Ferfesa Sabo ya ce za a gudanar da aikin ne a daukacin mazabu 11 tare da hadin kan sarakuna, shugabannin addini da na siyasa, matasa da kuma kungiyoyin mata.

Cikakken bayanin yadda Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Abba Kabir Yusuf

Shugaban ya kuma yi kira ga masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Bichi da su bada goyon baya a aikin da ke da nufin inganta lafiya da rayuwar al’ummar yankin baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...