Cikakken bayanin yadda Kotun daukaka kara ta yi watsi da karar Abba Kabir Yusuf

Date:

Khadija Abdullahi Aliyu

 

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya shigar na neman a yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta jihar Kano ta yanke.

 

Tawagar alkalan da suka hada da Justice Obande Ogbuiya, Williams Daudu da Ridwan Abdullahi a ranar Alhamis din da ta gabata sun bayyana cewa bukatar Abba Kabir Yusuf ta hana APC da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da wasu mutane biyu bada shaida bata da tushe ballantana makama.

Talla

Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara a kan amincewa da akai wani Dokta Aminu Idiris Harbau ya bayyana a kotun, don ya ba da shaida, Inda yace hakan kuskure ne.

Hotunan yadda Sabon Shatale-talen Kofar Gidan Gwamnatin Kano ya kasance

A cikin wasu dalilai guda shida na daukaka kara da lauyan gwamna Abba, Adegboyega Awomolo (SAN) ya bayar a gaban kotun, ya bayar da hujjar cewa alkalan kotun sauraron kararrakin zabe sun yi kuskure a shari’ar lokacin da suka amince da bukatar jam’iyyar APC ta bayar da izinin gabatar da wani shaida, Dokta Aminu Idris Harbau. Inda yace hakan ya sabawa tanadin sakin layi na 4(5) jadawalin farko na dokar zabe, 2022.

Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da cewa alkalan kotun sun yi kuskure tare da sabawa dokar zaben 2022, wajen baiwa shaidan damar bayyana a gaban kotu a matsayin shaida .

Al’ummar unguwar Danbare dake kano na kokawa da mawuyacin halin da titinsu ke ciki

Gwamnan ya kuma yi zargin cewa kotun da ke karkashin Mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ta yi kuskure tare da sabawa doka saboda ta amince da bukatar APC a lokacin da basu nemi Karin wa’adin ba inda ta yi amfani da karfinta wajen amincewa da bukatar.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito a ranar Litinin din data gabata ne kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan kano ta karkare karɓar bayani daga dukkanin bangarorin Shari’ar, inda ta yi alkawarin yanke hukunci kafin wa’adin da aka dibarwa kotun na kwanaki 18O ya cika.

Jam’iyyar APC ce dai ta shigar da karar inda suke kalubalantar hukumar INEC ta ayyana Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Aminu Dantata ya bar mana wasiyyar inda za a binne shi – Iyalansa

Iyalan marigayi Alhaji Aminu Alassan Dantata sun shaida cewa...

Da dumi-dumi: Ganduje ya yi murabus daga shugaban jam’iyyar APC na kasa

Daga Abdullahi Shu Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Umar...

Murtala Sule Garo Ya Taya Al’ummar Musulmi Barka da Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci ta 1447AH

    Tsohon dan takarar mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala...

Tinubu zai mayar da Fubara kan kujera gwamnan Rivers amma ya gindaya masa sharadi- Rahoto

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar...