Daga Hafsat Lawan Sheka
Sanatan kano ta kudu Hon Sulaiman Abdurrahman kawu Sumaila, OFR, ya kaddamar da daukar nauyin karatun dalibai guda dari 100 yan asalin yankin Kano ta kudu a wasu kwalejojin Lafiya masu zaman kansu guda biyar dake jihar Kano da jahar Jigawa.
Daga cikin matasan da suka rabauta da wannan tagomashi na karatu kyauta a makarantun kudi na Lafiya a jihar Kano, akwai mata guda 50 da Maza guda 50, baya ga wasu mabiya Addinin Kirista Guda Hudu wadanda dukkanninsu suka futo daga yankin na Kudancin Kano.

Da yake kaddamar da daukar nauyin dalibai a dakin taro na Central Hotel, Sanata Kawu Sumaila yaja hankalin wadannan dalibai da su tsaya tsayin daka wajan amfani da damar da suka Samu wajan samun ingantaccen ilimi.
Da dumi-dumi: NNPP Ta Maka Kwankwaso Kotu Bisa Zargin yiwa jam’iyyar Zagon Kasa
Ya kar da cewa an kashewa ko wane dalibai sama da naira dubu dari biyar a iya shekarar farko, yayinda dukkanninsu za’a kashe musu Naira Miliyan 135 a iya kudin makaranta na tsahon Shekaru uku daza suyi, sa’annan za’a rinka biyan kowane dalibi ko daliba naira dubu 10 kowane wata har zuwa lokacin da zasu kammala karatun nasu.
“Dama mun yi alkawarin idan Allah ya bamu dama irin wannan zamu yi amfani da abun da muke samu wajen inganta rayuwar matasanmu, musamman ta fuskar Ilimi da lafiya, to yanzu a yau zamu hada biyun duk a lokaci guda”. Kawu Sumaila
Inganta Ilimi: Kawu Sumaila ya Baiwa Wata Yarinya Gurbin Karatu a Jami’arsa ya Al-Istigama
” Mun shiga lungu da Sako na kananan hukumomin Kano ta kudu inda muka zabo matasa daban-daban wadanda zasu ci gajiyar rukunin farko na shirin tallafin karatu na waraka”. A cewar Kawu Sumaila
Wasu daga Cikin daliban da suka rabauta da samun wannan tagomashi na karatu kyauta sun bayyana farin Cikin su kamar haka.
Daga Cikin makarantun da Sanata Kawu ya dauki nauyin wadannan daliban gurbin karatu, Akwai Aminu Dabo College of Nursing, Da Emirates College of nursing dukan su a Nan Kano, dama wasu kwalejojin kiwon lafiya a garin dutsen jihar Jigawa, domin saukakawa daliban da suke da iyaka da jihar ta Jigawa, kamar Takai, Albasu, Ajingi da dai sauran su.