Daga Rukayya Abdullahi Maida
Dan gwagwaryar nan Kuma dan Siyasa Hon. Aliyu Harazimi Rano, yace abun da Sabuwar ministar Abuja Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta yi na kin baiwa shugaban kasa Tinubu hannu su gaisa ya sake fito da martabar jihar kano a idon duniya.

” Ka dubi alfarma irin ta Shugaban kasa wanda mutane da yawa sukan yi abun da bai dace ba don su faranta masa, amma a haka Mariya Bunkure ya Miko mata hannu su gaisa Amma taki bashi hannu saboda da tasan darajar kanta da Inda ta fito”.
Zanga-zanga haramun ce a addinin musulunci – Mal Dauda Lokon makera ya ƙalubalanci likitoci
Aliyu Harazimi Rano ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da jaridar kadaura24 a Kano.
Yace dama Mariya mace ce kamilallah wacce tasan mutuncin kansa da Inda ta fito, yace don haka tun da aka ayyana Sunanta a cikin jerin sunayen ministoci suke murna da farin ciki.
” Akwai da yawa matan aure da suke mantawa da aurensu da addinin su da Al’adar su su rika gaisawa da shugabanni, kaga ko tunda ita bata shita sahunta su ba, ai dole mu yaba mata Saboda mu Kara mata kwarin gwiwar cigaba da tsare mutuncin ta dana mutanen kano”. Inji Harazimi Rano
Hon. Aliyu Harazimi Rano wanda ya taba yin takarar shugabancin karamar hukumar Rano, ya ce suna da yaƙinin sabuwar Ministar garin abujan zata yi aiki tukuru don fitar da Ganduje da al’ummar jihar kano