Jarumi Aki ya bayyana dalilin da ya sa yake boye matarsa da ‘ya’yana ga shafukan sada zumunta

Date:

Daga Hafsat Lawan Sheka

 

Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Chinedu Ikedieze, wanda aka fi sani da Aki, ya bayyana dalilin da ya sa baya bari a ga iyalansa a shafukan sada zumunta.

 

Jarumin mai shekaru 45 a duniya ya ce ba ya so matarsa ​​da ‘ya’yansa su shiga shafukan sada zumunta saboda yana son su sami ‘yanci.

Talla

Ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da manema labarai .

Ya ce, “Ina da ‘ya’ya amma na yanke shawarar ajiye su a gefe saboda ni ne shahararren, ba su ba.

ECOWAS ta Sanya Ranar da Zata Fara Yakar Jamhoriyyar Nijar

“Ina so kawai su sami ‘yanci saboda duk lokacin da kowa ya san su, zai shafe su, kuma hakan zai sa su rasa ‘yanci, Kuma ba na son hakan.

“Don haka, na boye su har da matata, in ban da a sanarwar bikin aurenmu da aka ganta, kuma daga nan ba a kara ganin ta ba, hakan tasa take iya zuwa kasuwa, ta yi duk abun da take bukatar cikin yanci ba kamar ni ba.”

KADAURA24 ta tuna cewa Ikedieze ya auri masoyoyarsa Nneoma Nwaijah a shekarar 2011.

Ma’auratan sun haifi ‘ya’ya amma dan wasan ya yanke shawarar ɓoye takamaiman adadin ‘ya’yan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dalilin da ya sa na bar tafiyar Kwankwasiyya – Farouk Lawan

Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farouk Lawan, ya bayyana cewa...

An Dauke Shaikh Abduljabbar Daga Gidan Yari na Kurmawa Zuwa Wani Wuri – Yan uwansaba

Wani labari da ke yawo a kafafen sada zumunta...

Majalisu na neman sauya lokacin zabuka a Nigeria

Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Gabatar Da Kudirin Sauya...

Kungiyar Lauyoyi yan asalin jihar Kano sun mika korafi ga kasashen Amuruka Ingila da UN kan zargin kisan a Tudun Wada

Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano (National Forum of...