Ba Zamu Bari Yunkurin Juyin Mulki yayi Nasara a Nigeria ba – Rundunar Soji

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rundunar Sojin a Nijeriya ta ce akwai wasu marasa kishin ƙasa da ke zuga su, su kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya, wacce shugaba Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta.

 

Daraktan yaɗa labarai na rundunar, Birgediya-Janar Tukur Gusau ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya aike wa Daily Trust da sanyin safiyar yau Asabar, inda ya bayyana yunƙurin a matsayin rashin kishin ƙasa da kuma zalunci.

Talla

Sai dai kuma rundunar sojin ta ce wannan yunƙurin ba zai samu nasara ba duba da cewa sojoji na jin daɗin mulkin dimokuraɗiyya kuma za su yi duk me yiwuwa domin kare dimokradiyya a ƙasar.

Iftila’i Babban Masallacin Zazzau ya rufta ana sallah

A cewar Janar Gusau, sojoji za su ci gaba da aikin su da kundin tsarin mulki ya kallafa musu maimakon ɓata lokacinsu wajen yunƙurin kifar da gwamnatin dimokuraɗiyya wacce aka sha jan aiki wajen kafa ta, inda ya kara da cewa sojin Nijeriya ba za su kau da hankalin su wajen kokarin kare mutunci, martaba da zaman lafiyar ƙasar ba.

Wannan batu ya zo ne dai-dai lokacin da wasu ke kira da sojoji su karɓi ragamar mulki, inda a ganin su, dimokradiyya ta gaza.

A halin yanzu haka sojoji sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum a Nijer, inda ECOWAS ke fafutukar ganin an maido da gwamnatin dimokuraɗiyya a ƙasar dake makwabtaka da Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

“BAMA YI”: Kalma mai alamta tsayuwar alkiyamar raggo ko mutakabirin dansiyasa – Dr. Murtala Iliyasu Ayagi

  Daga Dr. Murtala Iliyasu Ayagi malamin a Kwalejin Koyar...

2027: Tinubu ya bayyana lokacin da zai ambata sunan wanda zai yi masa mataimaki

I'mFadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai...

Ciyaman din Wudil ya kaddamar da aikin gina magudanan ruwa a wasu garuruwa a yankin

Daga Maryam Adamu Mustapha   Shugaban karamar hukumar Wudil, Hon. Abba...