Zanga-zanga haramun ce a addinin musulunci – Mal Dauda Lokon makera ya ƙalubalanci likitoci

Date:

Daga Rahama Umar Kwaru

 

Wani malamin addinin musulunci a kano mai suna Malam Muhammad Dauda Lokon makera ya ƙalubalanci matakin da kungiyar likitoci masu neman kwarewa take shirin dauka na gudanar da zanga-zanga a ranar laraba mai zuwa, sakamakon rashin biyansu hakkokin su da gwamnatin da gaza.

 

” A addini musulunci zanga-zanga haramunce, saboda ana fakewa da ita wajen tada hatsaniya wadda ka iya kaiwa asarar rayuka da dukiyoyi, wanda kuma addinin musulunci ba ya goyon bayan duk wani abu da aka iya kaiwa wani ya rasa ransa”. Inji shi

Talla

Malam Dauda Lokon makera ya bayyana hakan ne lokacin da ke zantawa da wakilin Kadaura24 a Kano.

Ganduje ya bayyana dalilan da suka sa Tinubu ya cire sunan Maryam Shetty daga cikin Ministocin

Malam Dauda yace Maimakon zanga-zanga kamata yayi kungiyar likitocin ta bada damar zama a tebur domin warware matsalolinsu cikin kwanciyar hankali da lumana.

” Ku bi a hankali kar kuce dole sai an magance matsalolin ku cikin gaggawa, domin gaggawa daga shaidan take, kamar yadda Manzo Allah S A W ya fada a cikin Hadith, Kuma ku sani aikin ku aiki ne da dama Allah ya yi alkawarin baku sakamakonku a lahira ba duniya ba”. A cewar Malam Dauda Lokon makera

Talla

” Ina baku shawarar dakatar da wannan zanga-zangar da kuke shirin yi, domin idan ta jawo aka rasa rai to ku Allah zai kama ba kowa ba”‘. Inji shi

Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da ta Kara kaimi wajen cika alkawuran data daukar ‘ya’yan kungiyar duba da muhimmancin da aikin su yake da shi a cikin al’umma, don haka yace bai kamata a bari su shiga zanga-zangar ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan Amincewar Kasar Saudia , an Sanya Ranar Binne Aminu Dantata a Madina

Babban sakataren marigayi Alhaji Aminu Dantata, Mustapha Abdullahi Junaid...

Rashin Alhaji Aminu Dantata Babban Rashi ne ga harkokin kasuwanci a Duniya – Salbas

Daga Khadija Abdullahi Aliyu Babban kamfani a masana'antar mai a...

NNPPn Kano ta bayyana matsayar Kwankwaso kan batun yi wa Tinubu mataimaki a 2027

Shugabanin bangarori biyu na jam’iyyar NNPP a jihar Kano,...

A Gaggauce: Fadar shugaban Kasa ta musanta murabus din Sakataren gwamnatin tarayya

Daga Rahama Umar Kwaru Fadar shugaban Kasa ta musanta labarin...