Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Wata Kungiya mai zaman kanta mai suna Civil Society Legislative Advocacy Centre, CISLAC ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta fito da tsare-tsaren da zasu tabbatar da karin kudin harajin taba sigari a Najeriya.
Auwal Ibrahim Rafsanjani, Babban Darakta na CISLAC ne yayin wani taron manema labarai kan illlolin da hanyoyin da za’a yi amfani wajen dakile Shan taba sigari a Nigeria, wanda aka gudanar a Kano ranar Laraba.
Da yake yi wa manema labarai karin haske bayan shirin, Rafsanjani yace Tinubu a cikin manufofin da ya yi yaƙin neman zabe da su, ya yi alkawarin kara yawan kudaden kula da lafiya a kasar nan ta hanyar inganta kasafin kuɗi da kuma tantance harajin amfani da kayayyaki masu cutarwa irin su taba da barasa a matsayin hanyoyin da za’a yi amfani da su wajen samar da kudaden za’a inganta kuɗin kiwon lafiya a Nigeria .

Rafsanjani, wanda Solomon Adoga, Babban Jami’in Shirye-Shirye na CISLAC ya wakilta, ya tunatar da Shugaban muhimmancin cika wannan alkawari da yayi lokacin yakin neman zabe”, inda ya bukaci shugaban kasa da ya gaggauta aiwatar da shi.

Ya kara da cewa, musamman a lokacin da ya zamawar gwamnati wajibi daukar tsauraran matakai na tattalin arziki a kasa, wadanda suka sanya ‘yan kasar cikin mawuyacin hali da ba a taba ganin irinsa ba, akwai bukatar gwamnatin ta Kara kudaden haraji ga kayan da ke cutar da al’umma musamman taba sigari da barasa domin takaita masu shan tabar da marasa da kuma samar da karin kudaden ga fannin kula da lafiyar al’umma.
Juyin Mulki: Sojojin Nijar sun kama jami’an gwamnatin Bazoum har 180
“A cikin rahotonta na ci gaban Najeriya, Bankin Duniya ya lura cewa Najeriya za ta iya samar da sama da Naira biliyan 600 a duk shekara ta hanyar kara harajin kan taba da barasa.
“CISLAC na fatan tunatar da shugaban kasa wannan muhimmin alkawari da ya dauka yayin yakin neman zabe tare da rokon shugaban kasar da ya gaggauta samar da tsarin aiwatar da karin harajin taba sigari a Najeriya cikin gaggawa.
Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin tantace ma’aikatan REMASAB
“Dole ne a lura cewa, Najeriya na ci gaba da kasancewa a sahun gaba a kasuwancin tabar sigari a Afirka, inda matasa da yawan al’ummarta ke jan hankalin masana’antar ta taba. Dole ne gwamnati ta tashi tsaye don kare matasanta daga shan taba ta hanyar kara kudaden harajin Masana’antun dake Samar da sigarin inganta lafiyar al’umma da Kuma samar da kudaden harajin ga kasar nan”. in ji Rafsanjani.
Ya yi nuni da cewa shekaru da dama, CISLAC tana fafutukar inganta tsarin harajin taba sigari a Najeriya, yana mai cewa tsarin kara kudaden harajin taba ita ce hanyar mafi sauki da za’a takaita shan taba sigarin da kuma inganta tattalin arzikin kasa don al’umma su amfana.
“A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), tace shan taba sigari na kashe mutane akalla miliyan 6 a kowace shekara, kuma hakan na iya haura miliyan 8 nan da shekarar 2030 idan ba a shawo kan annobar ba a duniya. An kuma bayyana taba sigari a matsayin babban abin da ke kawo sama da kaso 80 cikin 100 na mace-mace da wuri daga cututtuka marasa yaduwa a cikin al’umma, WHO ta kuma yi kiyasin cewa ‘yan Najeriya 30,000 ne ke rasa rayukansu a duk shekara sakamakon cututtukan da taba ke haifarwa. Wannan ya zarce rayuka 3,000 da COVID-19 ta kashe a cikin shekaru uku na annobar.
“Bincike ya nuna cewa talakawa, musamman a kasashe masu karamin karfi suna kashe kusan kashi 10 cikin 100 na jimillar kudaden shigarsu kan taba sigari kadai, haka ya rage yawan kudaden da ake samu na sauran kayayyakin yau da kullun kamar abinci, ilimi da kiwon lafiya. Har ila yau, WHO ta bayyana cewa Shan tabar na ba da gudummawa ga rashin abinci mai gina jiki, kashe kudaden wajen neman lafiya” . Inji Rafsanjani
Yace Yadda harkokin kiwon lafiya yake cikin mawuyacin halin a Nigeria, akwai bukatar a kara kudaden harajin taba sigari da barasa domin yin da kudaden don inganta fannin lafiya da kuma takaita masu shan tabar a cikin Nigeria.