Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da shirye-shiryen mayar da rusasshen filin idi zuwa cibiyar harkokin addinin Musulunci ta ƙasa da ƙasa a jihar.
Kadaura24 ta rawaito Gwamnan Yusuf ya sanar da hakan ne a yayin taron buɗe-baki da malaman addini na jihar a jiya Asabar.

A yayin taron, Gwamna Yusuf ya bayyana shirin mayar da filin Sallar Idi na Kofar Mata zuwa cibiyar taron Musulunci ta kasa da kasa domin zama cibiyar gudanar da harkokin addini maimakon a bar shi a haka ba a amfani da shi sai shekara-shekara .
Ya jaddada cewa yayin da ake amfani da filin a halin yanzu sau biyu kawai a shekara, mayar da shi cibiyar addinin Musulunci mai daraja ta duniya zai samar da dauwamammen wuri na yada addinin Musulunci da kuma cudanya da ilimi.
Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu
Kuma bayyana cewa, an shirya gudanar da bikin aza harsashin ginin makwanni biyu bayan Sallar Idi, daga nan kuma za a mika cibiyar ga malamai domin gudanar da aikin.
Gwamnan ya kuma jaddada kudirin gwamnatin sa na gyara dukkan masallatan Juma’a a fadin jihar, tare da tabbatar da sun cika ka’idojin da suka dace na masu ibada.
Ya umurci kwamishinan harkokin addini da ya hada jerin masallatai da ke bukatar gyara cikin gaggawa domin gwamnati ta fara aikin su.