Daga Hafsat Lawan Sheka
Muƙaddashin babban sufeton ƴan sandan Najeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya bayana damuwa kan zanga-zangar da ƙungiyyin ƙadago suke shirya yi a duk fadin kasar, inda ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo rikici ba.
Rundunar ƴan sandan ta ce a baya irin wannan zanga-zangar ta kan rikiɗe ta zama tashin hankali, saboda haka ta ke gargaɗin cewa ba za ta bari a gudanar da duk wani abu da zai kawo matsalar tsaro ba.

A wata Sanarwar da kakakin rundunar ƴan sandan Najeriya, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, rundunar ta ce ƴan ƙasa suna da ƴancin yin zanga-zanga kamar yadda kundin mulki ya yi tanadi, amma dole ne a gudanar da ita cikin kwanciyar hankali.
Yajin aiki: Majalisar Dattawa za ta gana da gwamnatin tarayya da kungiyar ƙwadago
ACP Adejobi ya ce duk wani yunƙurin tayar da rikici a lokacin zanga-zangar ƙungiyar ƙwadago zai fuskanci fushin hukuma.
Ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya sun shirya fara zanga-zanga a faɗin ƙasar daga ranar Laraba 2 ga watan Agusta domin nuna rashin amincewa da soke tallafin mai da gwamnati ta yi.w ss