FIDA zata rubanya kokarinta wajen inganta Rayuwar mata da kananan yara a Nigeria

Date:

Daga abubakar zaharadden kano.

Kungiyar Lauyoyi Mata ta kasa FIDA reshen jihar Kano ta ce, zata tashi tsaye da rubanya kokarin da take wajen samar da ingantacciyar rayuwa ga mata da kananan yaran dake fuskantar kalubale a fadin kasar nan.

 

Shugabar Kungiyar a Kano Barr. Bilkisu Ibrahim Sulaiman, ce take bayyana hakan da safiyar wannan rana ga manema labarai yayin da Kungiyar ke tsaka da gudanar da taron da suka shirya domin samar da ci gaban mata da kananan yara a kasar nan.

Talla

Da take bayyana makasudin shirya taron, Biklisu Ibrahim ta ce, za su hada hannu da dukkanin bangarorin dake da karfin fada aji a fadin Nigeria don ganin al’umma sun gyaru.

Kotu ta tabbatar da Hanga a matsayin Sanatan Kano ta tsakiya, ta kori karar APC

Da yake zantawa da manema Labarai a gefen taron, tsohon Shugaban Kungiyar Lauyoyi ta kasa A.B Mahmud, ya yabawa Kungiyar ta FIDA kan yadda take gudanar da al’amuran ta a fadin Nigeria da nufin temakawa mata da kananan yara domin rage musu damuwa.

Barrister Aisha Faruk da Barrister Sa’adatu Mahmoud Ibrahim, na daga cikin Lauyoyi mata da suka halarci taron, da suke zantawa da yan’jaridu, sun bayyana yadda Mata da kananan Yara ke shan wahala a cikin Al’umma. Tare da tabbatar fa cewa a shirye suke domin mikawa gwamnatin abunda taron yakunsa

Taron dai ya samu halartar mai martaba Sarkin Kano Alh. Aminu Ado Bayero, wanda ya samu wakilcin Walin Kano Alh. Mahe Bashir Wali, da dai sauran manya na ciki da wajen kasar nan yayin da daga bisani aka rufe taron da Addu’a tare da fatan samun zaman lafiya anan Kano dama kasa baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi: Sarki Sanusi Fadi Matsayarsa Kan Hawan Sallah Babba

Daga Sani idris Mai waya   Mai Martaba Sarkin Kano na...

Sallah: Shugaban K/H Rano ya gargadi matasan yankin kan zaman lafiya

Daga Isa Ahmad Getso   Shugaban karamar hukumar Rano Malam Naziru...

Kansila a K/H Garum Mallam ya rabawa marayu 300 kayan Sallah

Daga Safiyanu Dantala Jobawa   Sama da yara mayaru 300 ne...