Daga Kamal Umar Kurna
Shugaban hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta jihar Kano Amb. Alhaji Ahmadu Haruna Zago, yace nan da mako guda al’ummar jihar kano za su shaida yadda hukumar sa zata kwashe dukkanin wata shara dake jibge akan titunan jihar domin gujewa ambaliayr ruwa.
“Duba da irin ayyukan da hukumar sa ta gudanar tun bayan daya karbi ragamar ta, al’ummar jihar Kano nada kyakkyawan zato da Sanya rai akan aikace aikacen a yanzu wanda hukumar tasa ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen share musu hawayensu”. Inji Danzago

Dan zago ya bayyana hakan lokacin da tawagar ‘yan jaridun dake aiki a gidan gwamnatin jihar Kano suka kai masa ziyarar aiki a ofishinsa.
Kotu ta tabbatar da Hanga a matsayin Sanatan Kano ta tsakiya, ta kori karar APC
Shugaban hukumar ta REMASAB ya bayyana hada hannu da ‘yan jaridu a matsayin wata saukakkiyar hanyar isar da Sako tare da tabbatar samun nasarar kowane aiki da aka Sanya a gaba.
Al’adun Bahaushe: Shin ko kun San Al’adar Bahaushe ta zuwa gida rainon ciki da haihuwa ?
Dan zago yace duba da cewa ‘yan jaridu wani yanki ne me girma da yake taka muhimmiyar rawar gani cikin al’umma, akwai bukatar akwai bukatar gwamnati da hukumomin ta suyi aiki dasu kafada da kafada domin cike gibin isar da Sako dake tsakanin kowace gwamnati da al’ummar ta.