Daga Safiyanu Dantala Jobawa
Sama da yara mayaru 300 ne su ka karbi tallafin suturu na maza da mata a karamar hukumar Garun mallam.
Da ya ke mika tallafin kansilan Noma na karamar hukumar Alh Abdurrashid Umar Dan’asabe Garun mallam ya ce sun rabawa marayun kayan ne duba da irin halin da wasu ke shiga na damuwa musamman a lokuntan bikin sallah ya sa ya ke bada gudunmawarsa ga marayu don rage masu damuwa.

” Wannan lokaci ne na farin ciki da ya kamata su ma yara marayu su kasance cikin farin ciki, kamar yadda yara masu iyaye suke kasancewa”. Dan asabe
Kansilan Noman, daga ya kuma bukaci sauran al’umma da su rinka daurewa daga dan abun da Allah ya huwace musu domin taimakawa marayun yankunansu.
Mariya Sani, na daya daga cikin wadan da suka karbi tallafin atamfa kuma ta godewa Kansilan Noma Abdurrashid bisa sa su cikin masu farin ciki a babbar sallah.
Daga cikin wadan da su ka halaci bikin bada tallafin akwai masu girma mataimakin shugaban karamar hukumar Alh Tasiu Sale Kwiwa da kansilolin karamar hukumar da malamai da sauran al’umma gari baki daya.