Sunayen Ministoci: Tsofaffin gwamnoni da yan takarda ne suka fi yawa cikin mutane 42 da Tinubu zai turawa Majalisa

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Yayin da ya rage kwanaki 20 wa’adin da kundin tsarin mulkin Nigeria ya baiwa shugaban kasa na nada ministoci ya cika, rahotanni na nuni da cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya tattara sunayen akalla mutane 42 da zai turawa Majalisar dattawa a wannan makon ko mako mai zuwa.

 

Sai dai an ga chanje-chanje na abubuwan da ba’a Saba gani ba a jerin sunayen, domin kunshin sunayen ya hada da ‘yan jam’iyyar APC dana babbar jam’iyyar adawa ta PDP da kuma wadansu wadan ‘yan takarda ne ba yan siyasa ba, wanda kuma ana ganin shugaban kasar yayin hakan ne a wani ɓangare na yin gwamnatin hadaka.

Talla

Jaridar The guardian ta rawaito Shugaban Tinubu ya zabo mutanen ne daga jihohi daban-daban ba tare da la’akari da jam’iyya ba, don su kasance cikin majalisar zartarwar ta kasa.

Yanzu-Yanzu: Shugaba Tinubu Ya Zama Shugaban ECOWAS

Yanzu haka dai kwanaki 20 ne cikin 60 suka ragewa Shugaban kasa don ya kafa majalisar zartarwarsa kamar yadda kundin tsarin mulkin Nigeria ya tanadar, sanann kuma ana sa ran Tinubu zai zabo ministocin a dukkanin jihohin Nigeria kamar yadda doka ta ce dole sai kowacce jiha ta sami wakilci a zauren majalisar zartarwar.

Rahotannin sun nuna cewa tsofaffin gwamnonin guda 5 ne kadai suka kasance a jerin sunayen, wanda a bayan an tsammaci fiye da haka .

Tsofaffin gwamnonin sun hadar da

1. Nasir El-Rufai (Kaduna)

2. Abdullahi Umar Ganduje (Kano)

3. Muhammad Badaru Abubakar (Jigawa)

4. Atiku Abubakar Bagudu ( Kebbi)

5. Nelson Wike ( Rivers)

Ga kuma sunayen wasu da aka ga sunayen su a jerin sunayen da za’a turawa majalisar Dattawa.

Sanata Gbenga Denial, kayode Fayemi sai Tokumbo abiru da Dr. Cairo Ojougboh sai Festus Keyamo , Victor Ndoma-Egba, Dr. Better edu, Sanata John Owan, Amb. Soni Abang, Akin Rocket, Ben akak.

Rahotanni da Majiyar Kadaura24 ta samu sun tabbatar da cewa yanzu haka dai an kammala tattara sunayen Kai ana jiran dawowa Shugaban kasa Bola Tinubu don ya tabbatar da su , sai a turawa majalisar dattawa domin tantancewa su.

An rantsar da shugaban Tinubu a ranar 29 ga watan mayu 2023 kwanaki 42 kenan , sai dai a wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban kasar Dele Alake ya fitar, yace shugaban zai nada ministocinsa ne cikin kwanaki 30 da kama aiki, sabanin yadda tsohuwar gwamnatin da ya gada ta kwashe watanni 6 ba tare da ta yi Ministocin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...