Cikin kwanaki biyar masu amfani da manhajar Thread sun kai miliyan 100

Date:

Ya zuwa yanzu Mutane sama da million ɗari ne suka yi rajista da Threads, sabon manhajar sada zumunta da aka kaddamar kwanaki biyar da suka wuce.

 

Wanna yana nufin Threads, wanda kamfanin Meta ya ƙaddamar, ya buge tarihin da aka kafa manhajar AI’s ChatGPT ya kafa a baya.

Talla

An sabuwar manhajar akan dandalin manhajojin Apple da Android a cikin ƙasashe 100 a ranar Larabar da ta gabata.

Sunayen Ministoci: Tsofaffin gwamnoni da yan takarda ne suka fi yawa cikin mutane 42 da Tinubu zai turawa Majalisa

Amma har yanzu manhajar ba ta kai Turai ba saboda rashin tabbas kan dokar sirrin bayanan EU.

 

Mark Zuckerberg, shugaban kamfanin Meta, wanda kuma ya mallaki Facebook, ya ce manhajar ta samu rijistar mutane miliyan 10 a cikin sa’o’i bakwai da kaddamar da ita kuma sama da miliyan 30 a safiyar Alhamis.

 

Sa’o’i 24 bayan haka, adadin mutane da suka yi rajistar amfani da manhajar ya ninka fiye da sau biyu.

Ina nan a Daura ban yi gudun hijira ba – Buhari.

A mabiya miliyan 100, a alkaluma da dandalin bayanai na Quiver Quantitative ya fitar, Threads ya kasance yan kasa da kashi ɗaya cikin uku na yawan mutane da ke amfani da Twitter.

BBC Hausa ta rawaito wasu masu amfani da shafin Twitter sun nuna rashin jin daɗi tun lokacin da Elon Musk ya karɓi kamfanin.

An kori ma’aikata da dama tun bayan da Musk ya sayi shafin, inda kuma ya sanar da sauye-sauye don taimakawa wajen samar da kuɗaɗen shiga a Twitter.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...

Bai dace ɗalibai su rika murnar kammala karatu ta hanyoyin da ba su dace ba – Mal Ibrahim Khalil

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa ‎ ‎ ‎Shugaban majalisar Malamai ta jihar Kano...

Budaddiyar Wasika ga Gwamnan Kano kan wanda zai maye gurbin Muhuyi Magaji R/gado daga Kungiyar Lauyoyi yan Kano

Zuwa ga Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf Gwamnan Jihar Kano Gidan...