Daga Rahama Umar Kwaru
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da nada Malam Aminu Ibrahim Daurawa a matsayin Kwamanda hukumar Hisba ta jiha.
Mataimakin gwamnan na musamman kan sabbin kafafen sadarwa na zamani, Salisu Hotoro, ne ya bayyana hakan a sashihin shafin sa na Facebook a yammacin wannan rana ta Litinin.

Sheikh Aminu Daurawa ya taba rike Mukamin lokacin mulkin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Kuma lokacin mulkin Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Sheikh Daurawa dai ya bar kujerar Kwamandan hukumar Hisbah ne bayan samun sabini na siyasa tsakaninsu da tsohon gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Malam Aminu Ibrahim Daurawa ne ya gudanar da tsarin auren zawarawa a hukumar lokacin da ya riƙe muƙamin a karon farko zamanin mulkin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.