Ya kamata ayi dokar da zata hana karya ka’idojin Hausa a allunan tallace – tallace – Dr. Saifullahi Dahiru

Date:

Daga. Aliyu Danbala gwarzo.

 

Kungiyar masu kishin harshen hausa ta Najeriya ta bukaci mahukunta da masu ruwa da tsaki a fannin harshen hausa dasu mai da hankali wajen tabbatar da ingantacciyar hausa musamman a allunan tallace-tallace kasancewar ana yiwa harshen hausa hawan kawara wanda hakan bai dace ba.

 

An bayyana hakan ne a yayin wani taro da kungiyar ta shirya a makarantar CERC dake gandun albasa a ranar Asabar, an yiwa taron taken , “Mafita a kan karya ka’idojin nahawun hausa a allunan tallace -tallace.

Talla

Farfesa Abdulkadir Dangambo shi ne ya gabatar da mukala a yayin taron ya kuma bayyana cewa ba dai-dai bane ace ana samun irin wadannan kurakuren musamman a nan kano kasancewar kano gari ne na hausawa wanda hakan cin fuskane ga hausawa.

Da dumi-dumi: Kamfanin KEDCO ya bayyana dalilin da yasa za’a rasa wuta a Kano

“Ina jin babu dadi idan Ina tafiya naga wani allan talla an yi ba dai-dai ba misali a lokacin da akasamu bullar cutar sarkewar nunfashi (covid19) duk allunan talla zaka ga ance ana iya daukar cutar ta hanyar (musabaka) wanda mu a harshen hausa musabiha muka sani ba musabaka ba.” Inji Farfesa Dangambo

Dr. Saifullahi Dahiru malami a jami’ar Bayero dake nan kano, yayi jawabinsa a kan hanyoyin da suka fi da cewa da abi domin samar da ingantacciyar hausa musamman a allon talla, daga cikin hanyoyin da suka dace a kwai bukatar a tanadi doka akan masu yiwa harshen Hausa karan tsaye.

Ya kara da cewar yana da kyau a ringa kiran taron karawa juna sani wanda zai hada da shugabannin kamfanoni da yan kasuwa da sauran masu alaka da Allunan talla a duk garuruwan hausawa .

Daga karshe yayi kira ga wannan kungiya dasu cigaba da bijiro da tsare-tsaren da zasu kawo wa harshen hausa cigaba a najeriya dama duniya baki daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...