Gwamnatin Sokoto ta kafa kwamiti don binkicen gwamnatin Tambuwal

Date:

Gwamnatin jihar Sokoto ta kafa wani kwamiti da zai bincike kan batun mallakar filaye da yadda aka sayar ko a ka yi gwamjon kadadrorin gwamnati a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar Sanata Aminu waziri Tambuwal.

 

Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Abubakar Bawa ya fitar, ya ce kwamitin mai mutane biyar ƙarƙashin jagorancin Justice M.A. Pindiga zai kuma duba asusun gwamnatin jihar domin gano adadin kuɗaɗen da aka samu sakamakon sayar da kadarorin.

Talla

BBC Hausa ta rawaito Sanarwar ta kara da cewa kwamitin zai kuma duba batun filayen da sabuwar gwamnatin ta ke zargin gwamnatin da ta shuɗen ta rabar ciki har da gidajen gwamnatin jihar da aka yi yi gwanjonsu.

Da dumi-dumi: Kamfanin KEDCO ya bayyana dalilin da yasa za’a rasa wuta a Kano

Haka kuma akwai batun motocin gwamnatin jihar da na kananan hukumomi.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗar da Barrister Nasiru Muhammed Binji a matsayin sakatare, sai Chief Jacob E. Ochidi, SAN, da Alhaji Usman Abubakar da kuma Barrister Lema Sambo Wali a matsayin mambobi.

An bai wa kwamitin watanni biyu domin gabatar da rahoton sakamkon bicikensa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Abin mamaki: Barawo ya sace Motar dake cikin ayarin motocin gidan gwamnatin Kano

Wani barawon mota ya kutsa cikin gidan gwamnatin jihar...

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...