Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Tsohon dan takarar dan majalisar tarayya a karamar hukumar Nasarawa, Barr. Ibrahim Isa Aliyu, ya bayyana nadin da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yiwa Hajiya Aminu Abdullahi Sani a matsayin kwamishina da cewa an ajiye kwarya a gurbinta.

” Babu shakka gwamnan jihar kano yayi zurfin tunani da har ya dauko Hajiya Amina ya bata wannan mukami, Saboda tana da kwarewa da gogewa a fannin aikin gwamnati, sannan kuma ta bada gagarumar gudunmawa wajen tafiyar kwankwasiyya a Nigeria da jihar kano baki daya.
Da dumi-dumi: Kamfanin KEDCO ya bayyana dalilin da yasa za’a rasa wuta a Kano
Barr. Ibrahim Isa ya bayyana hakan ne lokacin da ya je taya Hajiya Amina Abdullahi Sani murna bisa wanann mukamin da ta samu.
“Hajiya Amina dama can ta dauki dukkanin yan kwankwasiyya na karamar hukumar Nasarawa a matsayin ‘ya’yanta don haka Ina da kwarin gwiwar Hajiya zata taimaki yan kwankwasiyya sannan kuma ba zata baiwa gwamnan kano da jagoranmu na kwankwasiyya Kunya ba”. Inji Barr. Ibrahim Isa Aliyu
Barr. Ibrahim Isa wanda shi ne Matawallen Garin Gwagwarwa ya bukaci al’ummar karamar hukumar Nasarawa da jihar kano da su taya ta da addu’o’in samun nasara da kuma Allah ya bata ikon sauke nauyin da gwamna Abba Kabir Yusuf ya dora mata.
Hajiya Amina Abdullahi Sani wadda akafi sani da Amina HOD tana cikin mutane ukun da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya aikewa majalisar dokokin jihar kano sunayen su domin ta tantance su kuma ta amince masa ya nada su a matsayin kwamishinoninsa.
Tuni dai majalisar ta yi aikin da kundin tsarin mulkin Nigeria ya dora masu akan su , kuma har sun tantance su tare da amincewa gwamnan ya nada su a matsayin kwamishinoni .