Daga Kamal Yahaya Zakaria
Tsohon gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ce har yanzu bai samu takardar gayyatar da ake cewa hukumar karɓar korafe-korafe ta jihar kano ta aika masa ba.
Tsohon kwamishinan yada labaran na tsohuwar gwamnatin Ganduje Kwamarat Muhammad Garba ne ya bayyana hakan ga sashin Hausa na BBC.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito cewa hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano ta ce ta gayyaci tsohon Gwamna domin ya bayyana a gabanta don amsa tambayoyi kan faifan bidiyon Dala da ake zargin Gandujen yana karɓar cin hanci daga wajen yan kwangila.
DA dumi-dumi: Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano ta gayyaci Ganduje kan bidiyon Dala
Kuma dangane da sahihancin bidiyon da hukumar Muhyi take iƙirari, Muhd Garba ya ce ba za su ce uffan a kan wannan batu ba, don kuwa magana ce da take gaban kotu.
Umar Abdullahi Ganduje dai ya sha musanta zargin, inda ya riƙa iƙirarin cewa abokan adawa ne suka shirya maƙarƙashiya da nufin hana masa damar shiga zaɓen 2019.