Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Hukumar Korafe-korafe da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) ta gayyaci tsohon Gwamnan kano Abdullahi Umar Ganduje domin amsa tambayoyi kan faifan bidiyon dala.
A shekarar 2017, jaridar Daily Nigerian da ke wallafa labarin ta a yanar gizo, ta fitar da wasu faifan bidiyo na Ganduje da ake zargin yana karbar cin hanci daga hannun ‘yan kwangila.

A cikin faifan bidiyon, ana iya ganin shi yana sanya dalolin a cikin ajjihun farar babanrigarsa”.
Yadda Jam’iyyar APC ta Gabatar da Shaidu 5 Cikin 300 ga Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Gwamnan Kano
Ko da yake tun a wancan lokaci, tsohon gwamnan ya musanta zargin, yana mai cewa faifan bidiyon an kirrarsa kawai akai .
Abubawa 5 da aka cimma a zaman majalisar zartarwar Kano, bayan rantsar da Abba Gida-gida
Amma da yake jawabi a ranar Laraba a wajen wani taron kwana daya na jama’a kan ‘Yaki da cin hanci da rashawa a Kano’, Barr. Muhuyi Magaji Rimingado, ya ce an tabbatar da sahihancin bidiyon.
Daily trust ta rawaito da yake karin haske a wani taro a ranar Alhamis, Rimingado ya ce an gayyaci Ganduje domin zuwa don ya amsa