Ya kamata a samar da ofisoshin kungiyar bada shawarwari a jami’o’in Nigeria – Shugaban Jami’ar Bayero

Date:

Daga Umar Hussaini Mai hula

 

Shugaban jami’ar Bayero dake Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas yace akwai bukatar a samar da ofishin kungiyar bada shawarwari ga dalibai da malamai a duk jami’o’in Nigeria domin magance matsalolin karatu da dalibai suke shiga.

 

Kadaura24 ta rawaito Farfesa Sagir Adamu Abbas ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi bakuncin shugabannin kungiyar a ofishinsa, a wani ɓangare na shirye-shiryen gudanar da babban taron kungiyar a Kano.

Abubawa 5 da aka cimma a zaman majalisar zartarwar Kano, bayan rantsar da Abba Gida-gida

Yace kungiyar ta na taka muhimmiyar rawa wajen magance matsalolin Karatu da na iyali ga ɗalibai da malamai ta hanyar basu shawarwari masu nagarta a kowanne lokaci.

Talla

Farfesa Sagir Adamu ya kara da cewa a mafi yawan lokuta dalibai da malaman jami’o’i kan tsinci kawunansu a cikin matsaloli, to Amma idan aka Samar da ofishinsa kungiyar a dukkanin jami’o’in Nigeria hakan zai ragu, sannan kuma za’a sami cigaba Ilimi a Nigeria.

DA dumi-dumi: Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano ta gayyaci Ganduje kan bidiyon Dala

Da yake nasa jawabin shugaban kungiyar bada shawarwari ta kasa Farfesa Malami Umar Tambuwal yace sun zo Kano ne domin gudanar da babban taron kungiyar na kasa karo 47 a jami’ar Bayero dake jihar kano.

Farfesa Malami Tambuwal wanda shi ne shugaban jami’ar Ilimi ta Shehu Shagari ta jihar Sokoto yace kungiyar su tana iya bakin kokarinta waje magance matsaloli a cikin al’umma da kuma jami’o’i ta hanyar bada shawarwari don inganta rayuwar matasa da al’umma baki daya.

Yace kungiyar zata kwashe kwanaki biyar tana gudanar da taron ta na bana a Kano wanda za’a gudanar a cikin watan ogusta, kuma an yiwa taron na bana takan “tsaro da Muhimmancinsa ga al’umma”.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Zargin Almundahana: ICPC zata gurfanar da shugaban hukumar zabe ta Kano da wasu mutum biyu

    Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta (ICPC)...

Dalilin da ya hana ni zuwa Kano tarbar Tinubu – Ganduje

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa,...

Shugaban RATTAWU na Kano ya taya sabbin shugabannin kungiyar na kasa murna

Daga Aliyu Danbala Gwarzo   Shugaban kungiyar ma’aikatan rediyo, Talabijin da...

Dalilina na ziyartar gwamnan Kano Abba – Inuwa Waya

Daga Rahama Umar Kwaru Tsohon Wanda ya nemi Zama Dan...