Daga Nura Abubakar
Shugaban Hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano Barr. Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya ce ba zai tsaya duba abun da ya faru bayan ya bar hukumar ba , kawai zai maida hankali ne waje ciyar da hukumar gaba da kuma kwatowa al’umma hakkinsu.
Muhuyi Magaji Rimin Gado ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa bayan rakiyar da yan uwa da abokan arzikin su sukai masa .

Yace babu lokacin da zai tsaya yana rama abubuwan da akai masa a baya, duk da cewa yace bayan ya bar ofishin ya dawo ya iske an yi wata badakala, wadda kuma bazai bari ba saboda ba shi abun ya shafa ba.
Abba Gida-gida ya bayyana ma’aikatu ga sabbin kwamishinoni
” Gwamnan Kano Engr. Abba Kabir Yusuf ya bi umarnin kotu wajen dawo dani wannan matsayin don haka zan yi aiki tukuru don kara kare kambon wanann gidan na “Gatan mara Gata”. Inji Muhuyi
Shugaban hukumar karɓar korafe-korafe ta jihar kano, ya kara da cewa bayan dawowarsa hukumar ya fara bude wasu kararraki da aka shigar tun kafin tafiyar sa, amma yanzu ya fahimci akwai Almundahana da akai Inda aka nemi wasu matoci guda 7 da kuɗin ya akai Naira Miliyan 109 kuma ya rasa su.

” Ina so ku sani akwai abubuwan da dagayyama akai yi su don idan mun fara bincike ace ramuwar gayya ce, ba mu da lokacin ramuwar gayya, amma fa hakan ba yana nufin zamu zuba idan a cutar da al’ummar jihar kano ba ne, kawai don kar ace mun yi ramuwar gayya”.
Ya bada tabbacin zai kara kyautata alakar aiki da ma’aikatan hukumar da sauran al’umma domin sauke nauyin da aka dora masa na mayarwa mai hakki hakkinsa. Sanann ya bada tabbacin Muhuyi Magajin da aka Sani shi ne ya dawo zai kuma yi aiki bisa doron dokokin hukumar karɓar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar kano.