Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
Hukumar kula da aikin hajji ta kasa NAHCON, ta baiyana rashin jin daɗinta kan karancin tantanina ga wasu Alhazan Najeriya su dubu 10, a Muna, Wanda wani kanfanin kasar Saudiya ke aikin samar da Tantinan ga Alhazan Najeriya ya gaza sanarwa.
Shugaban hukumar, Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Muna, ya kuma ce bai ji dadin yadda aka tsara ciyar da alhazan a filin Muna ba, kasancewar abincin bai wadata ba, sannan kuma an kai abinchin ba akan lokaci ba.

” Tun da farko mun yi tunanin samun wannan matsala,wanda hakan tasa muka baiwa hukumomin saudiyya shawarar shigar dasu cikin tsarin ciyarwar mu, amma suka tilasta cewar suna da wani tsarin ciyarwa na bai daya”.Inji Zikirullah Hassan
Bani da lokacin batawa wajen ramuwar gayya – Muhuyi Magaji Rimin Gado
Shugaban hukumar ta NAHCON ya kara da cewa tuni suka sanar da ma’aikatar aikin hajji da umarah ta saudiya koken da Alhazan Najeriyar suka yi, domin daukar matakin da ya da ce.

Sai dai Shugaban kamfanin Mr. Sindhi ya nemi afuwar hukumar ta NAHCON da Alhazan Nigeria saboda gazawarsu wajen cikin alkawuran da suka yiwa alhazan Najeriya, sannan yayi alkawarin a kwanaki masu zuwa alhazan Najeriya zasu zamo cikin sahun farko da za’a fara baiwa abinchin.
Ya kuma ba da tabbacin zuwa karfe biyu na ranar wannan Laraba zasu samar da tantunan ga alhazai dubu 10 na Nigeria da suka rasa tantunan a jiya, inda yace hakan ta faru ne saboda Shirin kasar Saudiyya na rage cunkoso a filin na Muna