Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyarta na sake Gina sabon shataletale da ta rushe a hanyar shiga gidan gwamnati, zuwa hanyar kan titin gadar Sama dake Na’ibawa.
Bayanin Hakan ya fito ne daga gwamnan jihar Kano Engr.Abba Kabir Yusuf a yayin da ya ziyarci wurin da za’a sake ginin wanda suke tare da wadda ta yi zanan taswirar shataletalen kaltume Gana a Saban gurin da za a gudanar da wannan aiki.
” Sabon wurin da za’a sake gini dake nuna cikar Kano shekaru 50 ya ce sai yafi dacewa da wajen, kuma masana sun duba wajen sun tabbatar da cewa baza a sami wata matsala ba idan Akai gini a sabon wurin.

Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin jihar kano ta rushe shatale-talen dake Kofar gidan gwamnatin kano saboda dalilin tsaro da wasu dalilai da ta bayyana.
Hadiza Gabon ta Magantu kan batun kin auren Mutumin da ya kaita kara Kotu
A jawabinta wadda ta yi zanan taswirar ta ce hakika wajen ginin shataletalen ya dace zai Kuma kawatar da zarar an kammala aikin shi .
Ta Kuma godewa gwamnan jihar Kano bisa wannan dama da aka bata ta amfani da zanan taswirar da ta yi da jimawa