Na fara daukar matakai don warware yarjejeniyar jinginar da filin jirgin sama na Kano – Kawu Sumaila

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Sanatan kano ta kudu a zauren majalisar dattawan Nigeria Hon. Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya ce zai yi duk mai yiyuwa wajen ganin an warware yarjejeniyar da aka Ƙulla ta jinginar da filin jirgin sama na Malam Aminu kano dake Kano.

” Yanzu hakan na rubuta kudiri akan filin jirgin saman kuma na mikawa majalisar dattawa ta kuma karba, don haka ranar farko da muka koma majalisar zan mike domin gabatar da kuɗirin a zauren majalisar, don ganin an warware yarjejeniyar da aka kulla da wadanda suka karɓi jinginar filin jirgin sama”. Inji Kawu Sumaila

Dan majalisar dattawan ya bayyana hakan ne yayin wani shiri na musamman da gidan rediyon Freedom dake Kano suka yi da shi.

Tallah

“Gwamnatin da ta tafi ta jinginar da filin jirgin sama na Malam Aminu kano akan kudin Dala Miliyan daya da wani abu bata ma karasa Dala Miliyan 2 ba, kuma Shekarau hamsin aka ɗauka a yarjejeniyar , wanda duk sai mun mutu ba’a dawo mana da filin jirgin mu ba”. A cewar Kawu Sumaila

Kawu Sumaila ya nuna damuwa sosai kan yadda aka jinginar da filin jirgin, kasancewarsa filin jirgin sama na farko a Nigeria kuma inda jirgin sama ya fara sauka a Nigeria, sannan kuma garin wanda ya fara malllakar jirgin sama a Nigeria, don haka yace zai tabbatar da cewa an warware yarjejeniyar da aka Ƙulla a gwamnatin da ta gabata.

Abba Gida-gida zai sake gina Alamar cikar Kano shekaru 50 da ya rushe a Na’ibawa

Yace “da abun ba son rai a ciki ai da sai a jinginarwa da gwamnatin jihar kano filin jirgin saman tun da tana da kuɗin da zata iya karba jinginar, kuma zata iya kawo Kwararru da zasu yi gyare-gyare a filin, kaga da koma yaya za’a ce na kano ne, da na abuja ko na wani wajen ne, ka je kayi abun da duk kake so, amma banda a Kano”.

 

Dan majalisar dattawan na Kano ta kudu Sulaiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya sha alwashin indai yana majalisar dattawa sai yayi duk mai yiyuwa don ganin an warware waccan yarjejeniya ta jinginar da filin jirgin saman na Malam Aminu kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...