Daga Rahama Umar Kwaru
Sabon babban sufeton ‘yan sandan Najeriya na riƙo, Olukayode Adeolu Egbetokun ya ƙaddamar da abin da ya kira tsare-tsaren aiki don farfaɗo da yardar jama’a a kan ‘yan sanda.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ta ce a cikin manufofin babban sufeton akwai kafa jami’an kai ɗauki cikin hanzari mai taken Quick Intervention Squad wanda zai haɗar da ‘yan sandan kwantar da tarzoma da za su kasance shiri don kashe wutar fitintinu da aikata laifuka.
Binciken bidiyon Dala: Ganduje ya mayarwa Muhuyi Magaji Martani
Babban sufeton ya ƙaddamar da sabbin manufofin ne yayin wani taron ƙaddamar da salon shugabancinsa a shalkwatar ‘yan sanda ta ƙasa da ke Abuja.
Akwai fargabar gwamnatin Kano za ta rushe wasu gidajen Mai da rukunin shaguna a kano
Ya kuma ce shugabancinsa zai tabbatar da aiki da fasahohin zamani kamar ƙididdigar alƙaluma da harkokin tattara bayanan sirri don bunƙasa ƙwazon ‘yan sanda.
Haka kuma, babban sufeton zai tabbatar da aiki da wani tsarin martabawa da ba da lada don ƙara ƙwazo da ƙarfafa gwiwar jajirtattun jai’an rundunar. Yayin taron na ranar Juma’a manyan jami’an ‘yan sandan Najeriya daga faɗin ƙasar ne suka halarta.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ne a ranar Litinin ya naɗa sabbin hafsoshin tsaron ƙasar, a ciki har da Olukayode Egbetokun a matsayin babban sufeton ‘yan sanda na riƙo.