Daga Khadija Abdullahi Aliyu
Akwai fargabar gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Engr. Abba Kabir Yusuf zata rushe wasu gine-gine da aka yi su a gaban badalar dake kan titin zuwa tsohuwar jami’ar Bayero wato BUK Road a birnin kano.
Yanzu haka dai hukumar dake kula da tsara birane ta jihar kano KNUPDA ta Sanya Jan fenti a gine-ginen dake gaban badalar, wanda hakan ke alamta cewa kowanne lokaci daga yanzu za’a iya rushe gine-ginen.
Binciken bidiyon Dala: Ganduje ya mayarwa Muhuyi Magaji Martani
Kadaura24 ta gano Gidan Man Salbas dake kan titin zuwa tsohuwar jami’ar Bayero Kano, na cikin wuraren da hukumar tsara birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta sanyawa Jan Fenti.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito tun a makon farko na gwamnatin Abba Gida-gida ta fara rushe gine-ginen da tace anyi su ba bisa ƙa’ida ba.

Manyan Gine-ginen dake kan wancan wuri da za’a rushe akwai gidajen man Aliko Salbas da gine-ginen rukunin shaguna wato Plazas da dai sauransu.
Al’ummar jihar kano dai har yanzu na cigaba da bayyana mabanbanta ra’ayoyin su aka rushe gine-ginen da gwamnatin take yi.
A makon da ya gabata ne dai jaridar The Nation ta rawaito cewa daga fara aikin rushe gine-ginen an rushe gine-ginen da suka kai Naira Biliyan 126