Daga Aisha Aliyu Umar
Hukumar kula da aikin hajji ta Najeriya NAHCON ta gargadi maniyyatan Najeriya da su guji cin naman daji, fatu (ponmo), naman da aka gasa da sauransu saboda barkewar cutar anthrax a yankin yammacin Afirka.
Yanzu-Yanzu: Abba Gida-gida ya sake sabbin nade-naden mukamai
Kwamishinan lafiya na NAHCON Dr. Sa’id Ahmad Dumbulwa a wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce yin taka tsantsan ya zama dole duba da yadda ake gudanar da harkokin kasuwanci tsakanin kasashen Ghana, Togo da Burkina Faso, wanda kawo yanzu ya tabbatar da bullar cutar anthrax a kasar da wasu sassan yankunansu, da Najeriya.

“NAHCON tace ta zama wajibi a gargadi maniyyatan Nigeria saboda tsoron tuntubar zasu iya cudanya da yan wadancan kasashe, a yayin gudanar da aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya, wadanda duk da cewa ba lallai ba ne su kamu da cutar, amma don gudun kamuwa da cutar sai su ɗauki matakan kariya.