Daga Aisha Aliyu Umar
Akalla ministoci takwas ne aka gayyata wadanda suka yi aiki a karkashin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari kan zargin cin hanci da rashawa, kamar yadda majiyar hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta bayyana.
Wasikun gayyatan dai, an bayyana cewa, sun bukaci tsofaffin manyan jami’an gwamnatin na Buhari da su je su yi bayanin yadda suka kashe kudaden da aka ware wa ma’aikatun su a wasu ayyukan da suka gudanar a lokacin da suke rike mukamansu.
Rahotanni sun nuna cewa an rubuta wasikun ne zuwa ga tsoffin ministocin kafin a dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar.
Da dumi-dumi: Abba Gida-gida ya yi sabbin nade-naden mukamai
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta fara gudanar da bincike a kamar yadda wata Majiya dake cikin hukumar bayyana.
Kadan ya rage da na nada Aminu Ado a matsayin Sarkin Kano – Kwankwaso
Majiyar ta ce baya ga tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen, wadda aka gayyace ta a makon da ya gabata bisa zargin almundahanar Naira biliyan 2 da kuma “bangaren kudaden da ake zargin an karkatar da su daga aikin wanzar da zaman lafiya na uwargidan shugaban kasar Afrika,” an kuma gayyaci wasu kusan guda bakwai.
Idan dai ba a manta ba a watan da ya gabata ne hukumar ta kama Sale Mamman, wanda kuma tsohon ministan wutar lantarki ne a zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Buhari, tare da tsare shi bisa zargin almundahanar Naira biliyan 22 da ya shafi ayyukan wutar lantarki.
Hakazalika, an rawaito cewa tsohon ministan harkokin ‘yan sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, shi ma an gayyaci shi kan yadda ake tafiyar da asusun ‘yan sanda.