Daga Rahama Umar Kwaru
An zabi Tajudeen Abbas, dan majalisa mai wakiltar mazabar Zaria a matsayin shugaban majalisar wakilai ta 10.
Tajudeen Abbas ya samu kuri’u 353 inda ya doke abokan takararsa biyu Idris Ahmed Wase da Aminu Sani wanda ya samu kuri’u 3 kowanne.
Benjamin Kalu wanda ba shi da abokin hamayya , an bayyana shi a matsayin mataimakin kakakin majalisar.
Zababbun Mambobi dari uku da hamsin da tara ne suka kada kuri’a a yayin zaben shugabannin majalisr su biyu .
Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
An dai gudanar da zaɓen ne ta hanyar kada hanyar kada kuri’a kamar yadda doka ta 10 ta Majalisar ta tsara.
Tsohon Shugaban masu rinjaye na majalisar, Alhassan Ado-Doguwa ne ya gabatar da kuɗirin zabar sabon kakakin wanda Nnolim Nnaji mai wakiltar mazabar tarayya ta Nkanu ta Gabas/Nkanu ta Yamma kuma ya amince da shi.
Bayan kammala kada kuri’a wanda ya dauki sama da awa daya, magatakarda na majalisar wakilai Yahaya Danzaria ya sanar da Tajudeen Abbas a matsayin Shugaban Majalisar ta 10