Daga Halima Musa Sabaru
Dan mai wakiltar mazabar Rogo, a jihar kano Jibrin Falgore na jam’iyyar NNPP, ya zama kakakin majalisar dokokin jihar Kano karo na 10.
Yanzu-Yanzu: Akpabio ya zama Shugaban majalisar Dattawan Nigeria ta goma
Dan majalisar mai wakiltar karamar hukumar Dala, Lawal Hussaini, da Musa Kachako, mai wakiltar karamar hukumar Takai ne suka nuna sha’awar zabar Falgoren a matsayin Shugaban Majalisar dokokin jihar kano.
Kadaura24 ta ruwaito cewa Muhammad Butu-Butu shi ma ya zama mataimakin kakakin majalisar.
Daga nan ne magatakardar majalisar Alhaji Ali Maje ya rantsar da kakakin majalisar da mataimakinsa.
An dai zabi sabbin shugabannin majalisar ne bayan rantsar da majalisar ta goma.