Daga Nasiba Rabi’u Yusuf
An zabi dan takarar shugabancin majalisar dattawa da jam’iyyar APC ta tsayar , Godswill Akpabio a matsayin sabon shugaban majalisar dattawa ta goma.
Tsohon Gwamnan Akwa Ibom ya taba rike mukamin Ministan Harkokin Neja Delta daga 2019 zuwa 2022, yana wakiltar shiyyar Sanatan Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.
Abubuwan da ya kamata ku sani kan dokar ba wa ɗalibai bashin karatu a Najeriya
Akpabio dai ya kayar da abokin takarar sa ne Sanata Abduk’aziz Yari da kuri’u 63 yayin da yarin ya Sami kuri’u 46.
Jam’iyyar APC da shugaban kasa ne dai suka fito da akpabio a matsayin wanda suke so ya zama Shugaban majalisar Dattawa, yayin da shi kuma Abduk’aziz Yari ya ki janyewa dan takarar APC Inda ya nemi a shiga zabe a wannan rana da aka rantsar da majalisar dattawa.
Tunib dai Clark na majalisar, Sani Tambuwal ya rantsar da shi a matsayin Shugaban Majalisar Dattawan ta 10.