Zargin Almundahana: ‘Yan Sanda sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Zamfara

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta kai samame gidan tsohon Gwamnan jihar Zamfara Muhammad Bello Matawalle dake Gusau babban birnin jihar .

 

Rohotanni sun tabbatar da cewa an gano tare da kwashe motocin alfarma guda hudu a yayin samamen a gidan tsohon Gwamnan dake rukunin gidajen alfarma na GRA a juma’ar nan.

Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano

Majiyar Kadaura24 Daily trust ta rawaito har yanzu dai ba’a da tabbacin adadin motocin da aka gani a gidan, amma dai wata majiya ta tabbatar da an dauke motocin alfarma guda hudu a gidan.

 

Kokarin jin tabakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ASP Yazid Abubakar yaci tura.

 

Idan za’a iya tunawa Gwamn jihar Zamfara mai ci Dauda Lawal Dare ya zargi Matawalle da kashe tsabar kudi Naira Biliyan biyu da miliyan dari bakwai da casa’in da hudu da dubu Dari uku da talatin da bakwai (2,794,337,500.) wajen siyan motocin tawagar gwamna tare kuma dayin awon gaba dasu bayan barin mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rikicin gida: Jam’iyyar APC ta Fara Tuhumar Kakakinta na Kano Ahmad S Aruwa

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jam'iyyar APC ta Mazabar Daurawa a...

Iftila’i: An Sami Ambaliyar Ruwa a garin Maiguduri

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno...

Shugabanni ku rika gudanar da aiyukan da za su rage talauci a cikin al’umma – SKY

Daga Kamal Yakubu Ali   Fitaccen dan kasuwa a Kano Alhaji...

Muna da yakinin APC za ta lashe zabuka a Kano da Arewa don Tinubu ya yi tazarci a 2027 – Alfindiki

Jigo a jam’iyyar APCn Kano, Comrade Faizu Alfindiki, ya...