Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano

Date:

Daga Isa Ahmad Getso

 

Kotun sauraren kararrakin zabe ta Majalisar tarayya da jiha da ke zama a Kano, a ranar Laraba ta fara zaman share fage a wata kara da Musa Ilyasu Kwankwaso na APC ya shigar, yana kalubalantar ayyana Datti Yusuf Umar na NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar Kura/Madobi/Garun malan a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

 

Musa Ilyasu Kwankwaso yana rokon kotun da ta bayyana cewa Datti Yusuf Umar bai cancanta ya tsaya takara ba inda ya ce ya yi karya a lokacin da yake gabatar da bayanan karatun sa.

Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano

Ya kuma yi zargin cewa wanda ake kara bai ajiye aiki ba a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati har lokacin da ya tsaya takara, yana mai cewa hakan ya saba wa dokar zabe.

 

Musa Iliyasu ya kuma roki kotun da ta bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Kura Madobi/Garun Malan.

Kotu ta fara zama kan Shari’ar kujerar gwamnan Kano

Duk da haka, an fara zaman share fage ne da karɓar bayanaibayanai daga kowanne ɓangare kamar yadda yake a cikin fom TF007.

Hakazalika, an kammala tattara adadin shaidun da za a kira domin bada shaida a shara’ar.

Lauyan mai shigar da kara, Barista MN Duru ya shaida wa kotun cewa zai gabatar da shaidu 23 cikin kwanaki bakwai don tabbatar da zargin da ake yi wa wadanda ake kara.

A nasa bangaren, Lauyan hukumar INEC, Barista Abbas Haladu, ya shaida wa kotun cewa zai gabatar da shaidu 3 ne a kwanaki uku.

Yayin da Lauyan jam’iyyar NNPP ya shaidawa kotun cewa zai gabatar da shaida daya domin kare su.

Daga baya, Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Yuni 2023.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dr. Kabiru Getso Ya Mika Ta’aziyya Ga Iyalan Buhari

Daga Rahama Umar Gwaru   Tsohon kwamishinan ma'aikatun lafiya da muhalli...

Gwamnatin tarayya ta ayyana Ranar hutu saboda rasuwar Buhari

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana Talata, 15 ga watan...

Injiniya Iliyasu Usman Salihu ya zama Jakadan zaman Lafiya na Africa

    Injiniya Ilyasu Uasman Salihu, Manajan Darakta na Sadex Engineering...

Halin da ake ciki game da shirye-shiryen jana’izar Buhari

Gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, ya bayayna cewa sai...