Ba gudu ba ja da baya kan rushe gine-ginen da basa kan ka’ida a Kano– Gwamnatin Kano

Date:

Daga Khadija Abdullahi Aliyu

 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Comr. Aminu Abdussalam Gwarzo, ya jaddada kudirin gwamnatin Kano na ci gaba da rushe gine-ginen da aka yi su ba bisa ƙa’ida ba, kamar yadda gwamnatin ta faro .

 

Da yake jawabi a wata ganawa da mambobin kungiyar Progressive Tarauni karamar hukumar Tarauni a gidan gwamnati a jiya (Alhamis), mataimakin gwamnan ya jaddada mahimmancin bin doka da oda da kuma maido da oda a birnin kano .

Ba zan taba barin Masana’antar Kannywood ba har abada – Samira Ahmad

Abdussalam ya jaddada cewa wajibi ne rushe wadancan gine-gine domin tabbatar da ci gaban birnin kano da kuma kare muradun jama’a.

Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano

Da yake bayar da misalai, Mataimakin Gwamnan ya bayyana yadda gwamnatin da ta shude ta sayar da kadarorin jama’a domin amfanin kan sa, ba tare da la’akari da illar da hakan ke da ita ga al’umma ba. Ya bayyana sayar da filaye a Massalacin Waje mai dimbin tarihi a karamar hukumar Fagge da kuma wasu sassa na filin Idi, wadanda dukkansu suna da muhimmanci ga tarihi da al’umma da addininsu .

Abdussalam ya yi tsokaci game da shirun da masu adawa da sayar da kayan gwamnati musamman malaman addini suka yi a lokacin da tsohon gwamnan ke sayar da kadarorin gwamnati ga iyalansa da makusantansa. Ya kuma nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka sayar da wasu sassa na makabartu domin gina shaguna, yayin da ya jaddada kokarin da gwamnati mai ci ke yi na inganta irin wadannan wuraren.

Dangane da sansanin Alhazan, mataimakin gwamnan ya bayyana yadda aka raba kayayyakin da ke cikin sansanin da sayar da su, duk da manufar yin aikin a matsayin filin motsa jiki na alhazai. Sai dai ya bayyana cewa Gwamna mai ci Abba Kabir Yusuf ya dauki matakin sake gina sansanin tare da tabbatar da samar da ababen more rayuwa.

Mataimakin Gwamnan ya kuma yi tsokaci kan rushe Otel din Daula, wanda Marigayi Audu Bako ya kafa tun asali domin horar da dalibai a fannin yawon bude ido da kuma tsare-tsare. Ya nuna rashin jin dadinsa da yadda tsohon gwamnan ya rushe tsohon ginin tare da sayar da wurin ga iyalansa.

Kadarorin gwamnati da gwamnatin da ta shude ta siyar sun hada da gidan gwamnatin Kano da ke rukunin gidan Kwankwasiyya, ginin Triumph, filayen da ke kewaye da Jami’ar Yusuf Maitama Sule da dajin Dansoshiya, da manyan filayen noma na kananan hukumomi da dama.

Mataimakin Gwamnan ya tabbatarwa da daidaikun mutane da kungiyoyin masu ruwa da tsaki

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rasuwar Buhari: Majalisar Nigeria ta dakatar da duk aiyukanta

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Majalisar dokokin Nigeria ta dage zamanta...

Gwamnati ta baiwa ma’aikata hutu saboda rasuwar Muhammad Buhari

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Katsina karkashin gwamna Umar...

Bayan tura Kashim ya taho da gawar Buhari, Tinubu ya ba da umarnin sassauta Tutar Nigeria

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bada umarnin ayi kasa...

Yanzu:yanzu: Tsohon shugaban Nigeria Buhari ya rasu

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!! Allah yayi wa tsohon shugaban...