Daga Halima Musa Sabaru
Jarumar masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Samira Ahmad, ta bayyana cewa, duk da cewa ba ta fitowa a fina-finai a baya-bayan nan ba, amma tace har yanzu tana cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa.
Jarumar fina-finan, wacce kuma ta kasance mai shirya fina-finai, da ayyukan jin kai da kuma harkar kawata wurare ta kasance daya daga cikin fitattun jaruman Kannywood data shahara a chan baya, Samira Ahmad ta kasance ‘yar wasan kwaikwayo da kowane furodusa ke nema domin ya sakata a fim din sa .
Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano
Jarumar ta bayyana cewa babbar kawarta Mansura Isa, matar jarumin Kannywood kuma mawaki Sani Musa Danja ce ta shigar da ita harkar fim, inda ta kara da cewa tun da ta fara sana’ar ta zama gida a Masana’antar. Sai dai rashin fitowarta a fina-finai ya jefa masoyanta cikin zullumi tare da neman sani menene Dalilan da suka ta daina fitowa a fina-finai? hakan ce tasa muka tuntube ta don jin dalilan “Samirah Ahmed ta kada baki ta ce har yanzu tana cikin shirin Masana’antar Kannywood”.
Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano
An haifi Jaruma Samira Ahmad a ranar 24 ga watan Satumba a karamar hukumar Nassarawa ta jihar Kano a Najeriya; Samirah ta yi makarantar firamare ta Giginyu sannan ta wuce makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati a Kano. Bayan ta kammala makarantar sakandare ne jarumar ta shiga harkar shirya fina-finai sannan ta koma Kwalejin Ilimi ta Tarayya Kano (FCE) inda ta samu takardar shaidar difloma a fannin akanta da bincike.
Jarumar ta kuma bayyana cewa tana alfahari sosai da Masana’antar Kannywood, Inda Jarumar tace daina ganinta a fina-finai a yan shekarunan baya nufin ta daina harkar fim baki daya.
Ta kara da cewa ta samu alkhairai masu tarin yawa a harkar fina-finai don haka ta dan ja baya saboda wasu suma su zo don su sami abun da zai taimakesu wajen inganta rayuwarsu.
Jarumar wadda ta taka rawar gani a fina-finai kamar su ‘Sai na dawo, Garin dadi, Bissalam da Na Mamajo’ kuma rahotanni sun nuna cewa jarumar ta dauki nauyin dalibai sama da 100 domin yin karatu a cibiyoyin ilimi daban-daban sannan ta kuma gudanar da ayyukan samar da rijiyoyin burtsatse a makarantun sakandaren ‘yan mata da ke Jogana da dai sauransu.
An haifi Samira Ahmad a ranar 24 ga watan Satumba a jihar Kano inda ta taso tare da iyayenta.
Idan dai za a iya tunawa ta auri abokin aikinta TY Shaban wanda ya kasance mai Rawa, mawaki, kuma Furodusar Talabijin.
Auren Samira ya mutu bayan rashin rituwa da suka samu da mijinta.
Duk da cewa ta yi ritaya daga harkar fim har yanzu tana aiki a bayan fage.
Mafi rinjayen al’ummar Hausa/Fulani ne suka san ta bayan rawar da ta taka a fim din “Namamajo” inda ta kasance ‘yar karamar yarinya mai nakasa domin samun soyayyar ta ta gaskiya.
An tattaro cewa ba a taba korarta ko dakatar da ta ba a harkar fim.
Samira ta samu lambobin yabo da dama saboda bajintar da ta yi a harkar wasan kwaikwayo a Masana’antar Kannywood.