Daga Ali Danbala Gwarzo
Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumomin tsaro a Kano su dakatar da rushe shagunan da gwamnatin kano ke iƙirarin an gina ba bisa ƙa’ida ba.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fara rushe wasu gine-gene da gwamnatin dace gwamnatin Ganduje ta yi su ba bisa ƙa’ida ba.
Majiyar Kadaura24 Politics Digest ta rawaito cewar umarnin ya biyo bayan ganawar tsohon gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje da shugaban ƙasar a ranar litinin din data gabata.
Hukumar Kwastam ta Magantu kan sake bude bodojin Najeriya
Bola Tinubu ya bayyana rusau ɗin a matsayin abu maras ma’ana dake haddasawa ƴan ƙasa asarar da basu ji ba basu gani ba .
Ya umarci dukkanin hukumomin tsaro dake Kano da su tabbatar sun dakatar da rushe gine-gine a jihar kano.
Wata Majiya daga fadar shugaban kasa kace umarnin da shugaban kasa ya bayar shi yasa jiya da yau gwamnatin jihar kano bata yi rusau ba , domin jami’an tsaron sun bi umarnin Shugaban kasa.
Ko da Majiyar Kadaura24 ta tuntubi Mai magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa yace gwamnatin tana nan akan bakarta, na rushe duk wani gini da aka yi ba bisa ƙa’ida ba.
“Wannan aiki na muke (rusau) muna yin shi ne saboda al’umma jihar kano kuma zamu cigaba da yi har sai mun kau da duk wani gini da aka yi shi ba bisa ƙa’ida ba insha Allah”. Inji Sanusi Bature Dawakin Tofa