Daga Abdullahi Shu’aibu Hayewa
Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen Jihar Kano ta sake kama mutane 57 da zargin satar kayayyakin al’umma a matsayin ganima yayin da gwamnatin jihar ke rushe-rushen gine-gine.
A farkon makon nan ma rundunar ta kama wasu mutane, akasarinsu matasa, da zargin fasawa tare da sace kayayyaki a shagunan da ke ginin tsohuwar jaridar Triumph a ƙwaryar birnin Kano.
Kwankwaso ya nemi kotu ta kawace Nasarar wani dan majalisar tarayyar NNPP a Kano
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a yau Juma’a ta ce Kwamashinan ‘Yan Sanda Mohammed Usaini Gumel ne ya ba da umarnin yin fatiro babu dare ba rana don kare dukiyoyin mazauna jihar.
Da dumi-dumi: Bola Tinubu ya Magantu kan rushe gine-gine da gwamnatin Abba Gida-gida ke yi a Kano
Lamarin na faruwa ne yayin da sabuwar gwamnatin Kano ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta ke rushe gine-ginen da ta ce an yi su a kan filayen gwamnati ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta sayar.
A farkon makon nan wasu hotuna da bidiyo suka karaɗe shafukan sada zumunta, inda suke nuna wani gini yana ruftawa da matasa suna tsaka da ɗibar rodika da ƙarafa na wani gini da gwamnatin ta rushe.